Ko ya dace da aka dakatar da gina Cibiyar shirya fina-finai a Kano?

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta soke gina wani katafaren dandalin fina-finai wato Film billage a Jihar Kano. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan matakin ya yi daidai? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa: Matakin ya dace – Kabiru Mai Adashi Daga Hussaini Isah, Jos Alhaji […]

Ko ya dace da aka dakatar da gina Cibiyar shirya fina-finai a Kano?
Ko ya dace da aka dakatar da gina Cibiyar shirya fina-finai a Kano?

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta soke gina wani katafaren dandalin fina-finai wato Film billage a Jihar Kano. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan matakin ya yi daidai? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:

Matakin ya dace
– Kabiru Mai Adashi

Daga Hussaini Isah, Jos

Alhaji Kabiru Abdulsalam Mai Adashi: “Wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dakatar da aikin gina cibiyar shirya fina-finan Hausa a Kano  yayi daidai. Domin abubuwa da masu shirya fim din Hausa suke yi a fina-finan da suke shiryawa ya sabawa addininmu da al’adunmu. Abubuwan da suke nunawa dabi’u ne marasa kyau, don haka idan gwamnati ta gina wannan cibiya, kamar ta kara masu kwarin gwiwa ne, wajen ci gaba da gurbata mana al’ummarmu. Don haka wannan mataki da gwamnati ta dauka na dakatar da wannan aiki ya yi daidai, domin kamar ta ceto al’ummarmu ne daga ci gaba da fadawa cikin gurbatattun al’adu marasa kyau.

 

Ya yi daidai
– Manu Idris

Daga Hussaini Isah, Jos

Manu Isah Idris: “A gaskiya a ganina idan muka duba halin da muke ciki a kasar nan, soke wannan aiki na gina cibiyar  ya yi kyau. Domin akwai yara kanana ’yan mata da samari maza wadanda shekarunsu ba su wuce 18 zuwa  20 ba, har da matan aure suna tafiya wuraren da ake shirya irin wadannan fina-finai  suna yin abubuwan da ba su dace ba.  Idan aka gina masu wannan cibiya kamar an samar masu da wani wuri ne da za su ci gaba da yin abubuwan da ba su dace ba.  Kuma halin da muke ciki a Nijeriya yanzu, ba ta cibiyar shirya fina-finai ake yi ba. Don haka ya kamata a zuba kudin da aka ware don wannan aiki a wuraren da za a yi abubuwan da za su taimakawa al’umma  da gina kasar baki daya.

 

Ina goyon bayan dakatarwar
– Zulaihat Ahmad Akwaina

Daga Nasiru Bello, a Sakkwato

Zulaihat  Ahmad Akwaina:  “Malamai sun kyauta da wannan jihadin da suka yi na hana a gina alkaryar fina-finai a Kano. Ban goyon bayan  ci gaba da ginin, don ’yan fim suna gurbata tarbiyya ne ga yara kanana da manya. Wannan cibiyar za ta kara hadasa fasadi ne a jihar don kowa ya san halayyar ’yan wasa. Hakazalika, suna kara nuna rashin kamun kansu a wurin kalamai da suturar da suke amfani da ita. Gaskiya bai dace ba a yi wannan alkarya a Kano ba don ba harkar Musulunci ba ce ko al’ada.”

 

Matakin bai yi daidai ba – Yusuf Sarkin Yaki

Daga Nasiru Bello, a Sakkwato

Yusuf Sarkin Yaki: “Kodayake Hausawa sun ce ra’ayi riga.  A gaskiya bai dace da aka dakatar da ginin ba. Ya kamata malammai su dauke su tamkar ’ya’yansu na cikinsu ba wai a yi masu kallon wasu fasikai ba, marar tarbiyya. Ana fadar cewa idan an yi dandalin zai lalata tarbiyyar diyan mutane, amma ni ganina duk wanda ka gani ya lalace, tun fil azal lalatacce ne, bai samu tarbiyyar kwarai daga iyayensa ba. Wannan aikin a kasar Hausa, ba karamin ci gaba ba ne domin misali a ce za a shirya film a kan Tarihin Mujaddadi Shehu dan Fodiyo da sauransu.”

 

Soke ginin bai dace ba
– Ahmad Tijjani Ahmad

Daga Ahmed Ali, Kafanchan
 
Ahmad Tijjani Ahmad: “Tun da dai babu makawa sai an yi fim kuma ko a ina aka yi sai an kalla, zai fi kyau a bar gwamnati ta gina alkaryar. Bayan haka, sai a saka musu duk irin dokar da aka ga dama kamar na sauran kasashen Musulmi irinsu Iran, Masar, Turkiyya da kuma Saudiyya. Shin idan masu ruwa da tsaki a harkar fim ko wasu kungiyoyi suka gina musu irin wannan cibiya a wasu jihohi doka za ta yi tasiri a kansu kamar da a ce gwamnati ce ta gina musu? Koko dama gwamnati ba ta da manufa ko doka ne a kai? Adalci da shawara ya kamata a yiwa ’yan fim, ba munanan kalamai ba.”

 

Ya dace a gina Fim billage – Babangida Sa’idu Nuhu

Daga Ahmed Ali, Kafanchan
 
Babangida Sa’idu Nuhu: “Mutane sun jahilci alfanun da gina alkaryar fina-finai a Kano zai kawo ne ta fuskar bunkasar tattalin arziki ba wai a Jihar Kano kadai ba, har ma da Najeriya baki daya. Shi fa masana’antar fim reshe ne na adabi, ita kuwa al’umma ana gane ta ne ta hanyar adabinta, domin shi ne madubinta. To  me zai hana a yi musu gyare-gyare maimakon kyararsu! Na san korafin wasu malamai bai wuce su ce wasu kamfanonin shirya fim da ke masana’antar Kannywood ba sa wakiltar al’adun Hausawa ba, wannan haka ne, amma ai ba dukansu ba ne. Gina wannan cibiya a Kano a matsayinta na cibiyar fina-finan Hausa kuma gari mai dimbin al’umma zai samar da dubban ayyuka ga matasa, batun tarbiyya kuma ai kowacce sana’a na da gurbatattunta hatta ciki ’yan siyasa da malamai. ‘Ku Tashi Mu Farka ’Yan Arewa…’ mu ke adawa da ci gaban kanmu da kanmu sannan  mu zo muna dora w ’yan kudu laifin sun fi mu ci gaba.”