Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]

Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?
Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:

Taron bai dace ba – Adamu Juma
Adamu Juma: “Bai dace ba a halin da ake ciki, ba ma lokacin da za a ce ana maganar taron tattalin arziki ba ne saboda ana ta kashe mutane. Idan domin jama’a za a yi, yanzu ba abin da ya dace illa a nema wa mutane kwanciyar hankali ta kowane hali, ba kurum a yi ta kashe mutane ana kallo daga nan kuma a dawo ana kiran wasu taruka; ana raye-raye ana nuna rayukan jama’ar kasa ba su da wani tasiri a wajen shugabanni ba. Ba kasar da ke rayuwa ba tare da jama’a ba, to yau an wayi gari kullum ana kashe mutane, kowa yanzu ya dimauta game da abin da ke faruwa an zuba wa sarautar Allah ido, ana jiran taimakon Allah kan lamarin.”