Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?1

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]

Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?1
Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?1

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:

Taron bai da amfani – Yahuza Yusuf
Alhaji Yahuza Yusuf: “Ina ganin wannan taro ba shi da amfani, domin duk irin shawarwarin da aka zartar sai ko su amfani wasu kasashe na duniya amma ba za su amfanar da  Najeria ba, musamman ganin yadda a kullum ake ta kokarin ganin an shawo kan matsalar tsaro amma lamarin ya faskara. Ba wata kasa da za ta yarda ta zo domin zuba jari ko yin wata huldar tattalin arziki ta zahiri da Najeria, musamman ganin irin labarun da a kullum ake bazawa na kashe-kashe da sace mutane. Don haka a sanya matsalar kasa a gaba a magance komai ya fi alheri, kan a rika kashe kudi wajen karbar tarukan da ba za su yi amfani ba. Abin da ya fi dacewa shi ne, a maida hankali wajen gyara tattalin arzikin kasa da tsaronta tare da ganin an dawo da matan da aka kwashe kafin a kai ga kiran wasu daga waje kan wannan harka.”