Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?2

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]

Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?2
Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?2

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:

Lokacin yin taron bai yi ba – Yahaya Sawaba
Yahaya Sawaba: “A gaskiya taron bikin tattalin arziki na duniya da aka yi nan Naijeriya, akwai sauran lokacin yinsa, ba yanzu ne ya kamata ba saboda muna da kalubale a gabanmu na tashin hankula da wanzuwar arzikin kansa, taron da sun kai shi China ko wata kasa da ta ci gaba fiye da Najeriya da ya fi, amma kawai sai aka kawo shi matattar kasa da mutanenta ke cikin wahala. Ba ka san iyakar mutumin da ba ya cin abinci sau uku a rana ba, ka tambayi kanka in aka fada masa taron tattalin arziki za a yi, me kake zaton ya fadi? Ko kuma iyayen ’yan matan nan da ’yan Boko Haram suka kama za su gamsu da wannan taron, bayan sun san ba wani tatttalin arziki tun da aka kasa kubutar musu da yaransu, yau kusan wata guda ke nan suna cikin bakin ciki. Don haka ni ban ga ya kamata a yi wannan taron ba.