Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?3
A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]
A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:
Babu dacewa a taron – Sama’ila Mamman
Sama’ila Mamman: “Wannan taron bai dace ba, domin komai yana da lokacinsa; wannan taron ba lokacinsa ba ne, don a yanzu Najeriya na fuskantar matsalar tsaro sosai wadda ta fi ta kowace kasa a wurina. Taron tattalin arziki na duniya ya dace a yi shi amma ba a kasar nan ba, don duk inda ka ji maganar tattalin arziki to akwai arzikin a shimfide kuma duk inda akwai arziki a shimfide, to lallai za a samu zaman lafiya da lumana. A kasata Najeriya ba kwanciyar hankali kusan ko’ina a krewacin kasar, har a zo yin wani taron nishadi, to me ake son nunawa? Ba a damu da halin da ’yan uwanmu ke ciki ba ko kuma ana son a nuna mana kasarmu na da arziki? Sai dai bai amfani talakka ba, don haka masu mulkin da arzikin ya amfana, bari su zo su yi murna don ko tashin hankalin da muke ciki bai shafi masu mulki ba, mu ne talakawa kawai cikin matsi da kunci da halin kaka-ni-ka-yi.