Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?4

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]

Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?4
Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?4

A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:

Lokacin taron bai dace ba – Auwalu Suleiman
Alhaji Auwalu Suleiman: “Gaskiyar Magana, an yi shi a lokacin da bai dace ba, da aka yi shi a kasar da ake fama da rikici da tashe-tashen hankula da kuma rashin tsaro a kowace nahiyar Arewacin Najeriya, ana fama da ya za a dace a magance wannan matsala. Idan ma ya dace da sai an yi shi a Najeriya, to kamata ya yi a dage taron domin a san cewa akwai fa zaman juyayi na sace ’yan mata ’yan makaranta mako hudu ke nan da ake yi amma su shugabanni ba su damu ba sai suka mayar da hankalinsu kan abin da ya dame su. Shugabanni ba talakawa ba ne gabansu, mulki ne kawai gabansu domin ba su tunawa da hakkin talakawansu.”