Ko ya dace da aka gudanar da Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja a yayin da Najeriya ke cikin matsalar tsaro?5
A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har […]
A makon jiya ne aka gudanar da taron kwana uku a Abuja na tattalin arzikin duniya. An gudanar da taron ne a yayin da al’amuran tsaro suka sakwarkwace, inda ake juyayin sace ’yan mata kusan 300 da Boko Haram suka yi, ake kuma ci gaba da juyayin harin bam da aka kai garin Nyanya har sau biyu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace da aka gudanar da wannan taro na duniya, a yayin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro? Ga abin da wadanda aka tuntuba suka bayyana dangane da haka:
Gudanar da taron bai dace ba – Isyaka Muhammad
Alhaji Isyaka Muhammad Hadeja: “Ai bai ma dace a yi taron nan ba, kamata ya yi a yi zaman jimamin kama ’yan matan Chibok da wasu ’yan bindiga suka yi mako hudu ke nan. Abu ne fa wanda ya daga wa kasashen duniya hankali, ake ta zanga-zanga a kai; su kuma shugabannin kasarmu Najeriya, ga abu ya faru a kasarmu har ma sauran kasashen duniya na taya mu jimami; sai ma kawai suka tsaya suna gudanar da taron tattalin arzikin kasashen duniya, mai makon a mayar da hankali wajen ceto yaran nan.”