Ko ya dace gwamnati ta rika rangwamen canjin Dala ga masu tafiya Hajji ko Isra’ila a duk shekara?

Ganin ake ta koka wa da yadda kudin Hajjin bana ya tsada, da sanarwar da Majalisar Dattijai ta fitar a kwanan nan inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta bayar da rangwame ga masu tafiya hajji ta hanyar samar musu da canjin dala a kan Naira 200 a kan dala daya. Wasu sun yi maraba da […]

Ko ya dace gwamnati ta rika rangwamen canjin Dala ga masu tafiya Hajji ko Isra’ila a duk shekara?

Ganin ake ta koka wa da yadda kudin Hajjin bana ya tsada, da sanarwar da Majalisar Dattijai ta fitar a kwanan nan inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta bayar da rangwame ga masu tafiya hajji ta hanyar samar musu da canjin dala a kan Naira 200 a kan dala daya. Wasu sun yi maraba da wannan kira ta Majalisar, yayin da wasu kume suke ganin bai kamata ba. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin tab akin mutane, kuma ga abin da suke cewa:

 

Bai dace ba – Shehu Gajo

Daga Umar Mohammed Gombe, Abuja

Alhaji Almudo Shehu Gajo: “Gaskiya bai dace Gwamnatin Najeriya ta ba maniyyata rangwamen canjin dala ba, domin akwai mabukatan tallafin dala fiye da masu aikin hajji da zuwa Isra’ila. Sanin kowa ne cewa aikin hajji da zuwa Israi’ila na masu iko ne kamar yadda yake a Musulunci. Wannan iko ya hada da tanadin isashshen guzuri, samun ingattacciyar lafiya, samun hanya mai tsaro da kuma barwa iyali wadataccen kudi don gudanar da al’amuran yau da kullum. Don haka nauyin aikin hajji ko zuwa Israi’la ya ta’allaka ne akan maniyyaci ba gwamnati ba. Shi yasa yawancin kasashen musulmai na duniya ‘yan kasuwa da kungiyoyin addini ne suke gudanar da wannan aikin a kasashen su.Domin yawan dala a baitul malin kasa da kasa shine ginshikin tattalin arzikin kowace kasa a duniya. Kuma dala ce ake amfani don hada-hadar yau da kullum a fadin duniya. Don haka kasashen duniya suna takatsantsan a fannonin da suke amfani da dalar.” 

 

 

Rangwamen yana da amfani  – Mujitaba

Daga Abubakar AbdurRahman Dodo a Kano

Mujitaba Muhammad Namadi: Iyakar rayuwata a kofar Waikla cikin birnin Kano ban san wani abin da talaka ke karuwa da shi kai tsaye daga gwamnati ba a ’yan shekarun nan, tunda a da an amfana da ruwa da wuta da makaranta da asibiti. Domin makarantun gwamnati ma suna da inganci, sannan asibiti ba sai ka biya kudin ganin likita ko na magani ba. Bisa la’akari da wadannan dalilan ina ganin lallai a taimaka wa alhazai masu zuwa aikin hajji da canji kudi mafi karanci na Naira 200 kan kowace dala. Idan an yi haka za su san cewa sun amfana daga gwamnatin  kasar su, kuma sun samu karuwa ta ci gaba tunda sua daya ne a shekara kawai. Sannan su ma Kiristocin ’yan kasa sun canci a yi musu irin wannan don su samu karuwa ta kai tsaye da gwamnati. Idan kuwa har gwam nati ta tsdaya kan bakanta cewa ba a ta bayar da canjin Dalar kan Naira 200 ga mahajjata ba, to a bullo da karuwa ko wasu ayyuka da za su inganta rayuwa ko kyutata walwala da jin dadin al’ummart kasar nan kai tsaye.

 

 

Yana da kyau a rika yin rangwame 

–Malam Kabir Adamu

Isiyaku Muhammed

Malam Kabir Adamu: Gaskiya yana da kyau a rika yi wa maniyyata rangwamne wajen canjin dala. Wasu talakawa ne, kuma suna son su je su sauke farali, idan dala ta yi tsada, zai yi wuya su iya zuwa. Wannan shekarar limamin anguwar mu yana ji yana gani ya fasa zuwa hajji saboda kudin ya yi tsada, duk da cewa da farko ya yi niyyar zuwa. Don haka ina goyon baya a rika bayar da rangwame domin mutane su samu sauki.

 

 

Bai kamata a maida bukatar mahajjata bukatar kasa ba – Dakta Almuhajir

Daga Umar Mohammed Gombe, Abuja

Dakta Sheriff Almuhajir: “Wannan tattaunawa ta mun matashiya akan zantawar da na gabatar a gidan radiyo na muryar Amrukaakan sabon tsarin Najeriya na sake farashin dala ga kasuwanni.Lura da cewa Najeriya kasa ce dake dogara kan abubuwan da aka sarrafa a kasashen ketare. Don haka bai kamata gwamnati ta maida bukatar mahajjata zuwa bukatar kasa ba. Saboda ita wannan ibadah tana daka’idarta ga dukkan wanda yay i niyyar zuwa.Dole sai kana da wadatar daukar nauyinta. Duk wanda ba shi da wadataccen iko ta sauka akan shi. Zan so ace maimakon gwamnati ta tallafa cikin abinda bai karawa talaka komai, kuma ya baiwa ma su hannu da shuni amfani da kason dukiyar talaka, gara ta maida hankali wajen dawo da tsohon tsarinta na bada tallafi ga farashin dalar baki daya, saboda amfanin hakan zai rage wahalhalu da hauhawar farashi a kasuwannin mu, amma ba bangare daya ba.” 

 

 

Na goyi bayan canjin Dala kan 200 ga Alhazai – Abubakar Malumfashi

Daga Abubakar AbdurRahman Dodo a Abuja

Abubakar Hassan Malumfashi: Ina goyon bayan gwamnati ta bai wa alhazai canjin Dala a kan Naira 200, domin wannan zai kara musu kwarin gwiwa wajen yi wa kasa da shugabanni addu’o’i nagari. Duk kuma mai addini day a yi imani da Mahalicci Allah matukar aka taimaka masa ya samu sauki wajen gudanar da harkoki ko ayyukan ibada sau daya a shekara kawai ni ban ga wania bin tayar da jijiyar wuya. Kuma su ma Kiristoci idan har lokacin ziyarar ibadarsu ya zo sai gwamnati ta duba yiwuwar irin wannan karimci don kasa ta zauna lafiya, ta yadda babu wanda zai ce an nuna masa bambanci. Babbar manufa dai kasa ta zauna lafiya, a yi duk abin da za a bai wa al’umma kwarin gwiwa su ci gab a da yi wa kasarsu fatan alheri. Wannan ne dalilin da na dogara das hi na goyon bayan a bayar da canjin Dala ga alhazanmu kan Naira 200.

 

A rika tallafa wa wandanda za su je na farko – Auwal Adamu

Isiyaku Muhammed

Auwal Adamu: Gaskiya yin rangwamen na da amfani matuka, amma sai dai ni a tunani na, ya kamata a rika yin rangwamne ga wadanda za su je a karon farko, domin shi ne wajibi. Amma idan mutum zai koma ne, to kada a masa rangwame domin ba dole bane. Gara ma ya tsaya ya tallafa wa mutanen garinsu da kudin zai fi muhimmanci.