Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Yi wa zawarawa aure bai dace ba -Bala Adamu BoltungoMalam Bala Adamu Boltungo: Ina ganin yi […]
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:
Yi wa zawarawa aure bai dace ba -Bala Adamu Boltungo
Malam Bala Adamu Boltungo: Ina ganin yi wa zawarawa aure da gwamnati take yi bai dace ba, saboda (in) ita gwamnati da gaske take yi, wasu zawarawan kuma jari suke nema. Ma’ana suna yin auren ne don wannan kayan auren da ake yi. Amma kuma da zawarawan za su yarda su yi auren (da gaske), wasu (kuma) su koma gidajen mazajensu na farko da hakan zai kawo saukin tarbiyyar ’ya’yan da suka fita suka bari a hannun kishiyoyinsu.
Wata fuskar kuma ta inda bai dace ba din ita ce ana kara samun wasu magidanta suna hada baki tsakanin mata da mijin su ce aurensu ya mutu, mijin ya koma ya kawo matar tasa a matsayin bazawara don a sake daura musu aure, ka ga hakan cin amana ne.
A don haka ina kira ga gwamanti, idan ta aurar da zawarawa, su kuma ’yan mata, wadanda su ne suka fi yawa, yaya za a yi da su?