Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?1
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Yi wa zawarawa aure ya dace idan… -Hedmasta Ibrahim SizaMalam Ibrahim Siza (Hedmasta): Yi wa zawarawa […]
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:
Yi wa zawarawa aure ya dace idan… -Hedmasta Ibrahim Siza
Malam Ibrahim Siza (Hedmasta): Yi wa zawarawa aure ya yi daidai muddin za a bi tsarin da addinin Musulunci ya koyar na yin aure. Da yawa za ka ga bazawara ko bazawari na da bukatar yin aure, amma ba su da kudin yin auren, idan gwamnati ta yi musu, tunda kowa shi yake kawo wanda yake so, ka ga za a zauna lafiya.
Aurar da zawarawa alheri ne, domin idan suna gidajen mazajensu babu wacce zat a dinga bibiyar, musamman ’yan siyasa, har ta kai ga wata ta sayar da ’yancinta a kan kudin da ba zai rufa mata asiri ba.
Sannan kuma ina cewa duk wanda ya taimaka aka yi aure don raya sunnar Manzon Allah (S.A.W) yana da rabo mai yawa. Ka ga ashe gwamnati tana yin aikin da Allah Yake so ne ke nan.