Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?2

Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta  rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?  Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Ba gwamnatocin jihohi ba, attajirai ma su ba da gudunmawa -Alhaji Salisu dan ArewaAlhaji Salisu dan […]

Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?2
Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?2

Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta  rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?  Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:

Ba gwamnatocin jihohi ba, attajirai ma su ba da gudunmawa -Alhaji Salisu dan Arewa
Alhaji Salisu dan Arewa da ke Sabo Ibadan:  Abu ne mai kyawun gaske sauran gwamnonin jihohi su yi koyi da Jihar Kano wajen kafa hukumar samar da mazajen aure ga zawarawa. Idan suka aiwatar da hakan, to sun taimaka wa zawarawan kuma sun taimaki kansu ne. Idan ma ba su da kudi da za su iya yin kamar na Kano, to su yi shi daidai ruwa daidai kurji. Kuma attajirai masu hannu da shuni su bayar da tasu gudunmawar domin a cimma wannan buri a kowace jiha. Amfanin haka yana da yawan gaske, musamman zai rage yawan yawon zinace-zinace da wasu matan ke yi a dalilin kasa hakuri.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya