Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?3
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Yana da kyau gwamnatoci su taimaka wa zawarawa, amma… -Rabaran ElokedeRabaran Elokede Tae, ta cocin CAC, […]
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:
Yana da kyau gwamnatoci su taimaka wa zawarawa, amma… -Rabaran Elokede
Rabaran Elokede Tae, ta cocin CAC, Mokola Ibadan: Yana da kyau sauran gwamnatocin jihohi su yi koyi da Jihar Kano, wajen taimaka wa mata ’yan uwana zawarawa samun mazajen aure. Wannan babu laifi, amma ya kamata a canza irin tsarin da ake yi wajen daura aure a tsakanin ma’auratan. Kamata ya yi a yi koyi da salon yin amfani da gidajen talabijin da jihohin Kudu suke yi wajen kulla hanyoyin ganawa a tsakanin bazawara da masoyinta da za su gana da juna a gaban ma’aikatan da suka yi shirin, idan suna son juna sai a nuna su a cikin talabijin kuma a tsayar da ranar aure. Wannan zai ba su damar samun lokaci domin sanin halin juna. Amma irin tsarin da ake yi a Arewacin kasa, yana son gyara domin gajeren lokacin tadi a tsakaninsu yana haifar da rabuwarsu cikin kankanen lokaci, ka ga an koma gidan jiya ke nan.