Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?4
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Yana da kyau a ci gaba da shirin -Salihu Adamu Salihu Adamu: ‘’Babu shakka ina goyon […]
Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano? Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:
Yana da kyau a ci gaba da shirin -Salihu Adamu
Salihu Adamu: ‘’Babu shakka ina goyon bayan shirin, dari bisa dari, saboda haka ya dace a ci gaba da aiwatar da shi domin a halin gaskiya tsadar kudin aure yake hana maza da dama su yi aure. Don haka wannan shirin babu wani kushewa a ciki, taimako ne babba da Allah Ya kawo wa maza da mata domin yawan mata marasa aure cikin al’umma fitina ce babba.
Shawara a nan ya kamata a ce gwamnati ta shigar da likitoci cikin shirin, sannan kuma ta bi tana tallafa wa irin wadannan mazajen da abin da za su kulla sana’a da shi. Ina gani muddin gwamnatin ta yi wannan, zai kara wa shirin armashi sosai.