Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?5

Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta  rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?  Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka: Shirin ya dace  a ci gaba da shi -Ibrahim Muhammed Ibrahim Muhammed Sumaila: Wannan shirin a […]

Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?5
Ko ya dace gwamnati ta rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?5

Zauren Mahawara ya leka wasu daga cikin sassan kasar nan don jin ra’ayin jama’a a kan ko ya dace gwamnati ta  rika yi wa zawarawa aure kamar yadda ake yi a Kano?  Ga ra’ayin kowane daga cikinsu kamar haka:

Shirin ya dace  a ci gaba da shi -Ibrahim Muhammed

Ibrahim Muhammed Sumaila: Wannan shirin a gaskiya yana da kyau kuma  ya dace a ci gaba da shi a ko’ina cikin kasar nan. Aurar da wadannan zaurawan ba karamin taimako ba ne ga maza marasa galihu da matan kansu kuma tamkar kariya da rufa wa irin wadannan matan asiri ne.
Sai dai kuma shawarar da zan bayar a nan ita ce ya kamata malaman addini su ci gaba da  fadakar da jama’a muhimmacin shirin a addinance, sannan kuma ita gwamnatin ta sa masu kula da shirin suna sa ido sosai domin bata-gari da za su shigo da nufin dibar ganima, alhali su ba zaurawa ba ne suna da aure.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya