Ko ya dace Gwamnatin Buhari ta canza kudin Najeriya?

Wasu na ganin cewa muddin gwamnati na son samun nasara a yakinta na hana cin hanci da rashawa da satar dukiyar al’umma sai ta dauki mataki, ta canza kudin kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Buhari ta canza kudin Najeriya? Ga abin da mutane ke cewa: Halima A. […]

Ko ya dace Gwamnatin Buhari ta canza kudin Najeriya?
Ko ya dace Gwamnatin Buhari ta canza kudin Najeriya?

Wasu na ganin cewa muddin gwamnati na son samun nasara a yakinta na hana cin hanci da rashawa da satar dukiyar al’umma sai ta dauki mataki, ta canza kudin kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Buhari ta canza kudin Najeriya? Ga abin da mutane ke cewa:

Halima A. Musa, a Abuja

Hajiya Balikisu Salis Khalid: “Ni daman yanayin kudin nan namu ba ya burge ni, gara a canza; a samu masu ’yan daraja kuma cin hancin da rashawa shi ke ci mana tuwo a kwarya, don haka a canza kawai.”

Ina goyon bayan canja kudi – Auwallu Sharubutu

Hussaini Isah, a Jos

Auwallu Sharubutu Mai siminti: ‘’A ra’ayina, ya dace a canza kudin Najeriya, domin idan aka yi haka za a yi maganin barayin da suka sace kudaden Nijeriya a lokacin gwamnatin da ta gabata. Domin da dama irin wadannan barayi da suka sace kudaden Nijeriya, sun ajiye su a gidajensu. Idan aka canza kudaden abin zai zamo masu tashin hankali. Kuma ’yan Najeriya da dama ba su son wasu kudaden da ake amfani da su a halin yanzu. Don haka canza kudaden zai yi daidai.”

A canza kudin idan… Jamila Madaki

Halima A. Musa, a Abuja

Malama Jamila Madaki: “A gaskiya idan har canza kudin mu zai taimaka wurin shawo kan cin hancin nan da rashawa, muna masu ba da goyon bayan mu dari-bisa-dari.”

Canza kudin zai yi amfani – Dauda Modu

Sani Gazas Chinade

Malam Dauda Modu: “A nawa ganin, canza kudin kasar nan shi ya fi alfanu, domin kuwa in an yi hakan za a yi maganin ire-iren shugabannin da suka kwashi kudadenmu suka tara don tsira da talaucin duniya kamar yadda suke fada. Har ila yau in har sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta canza kudaden kasar nan, akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar ya bunkasa fiye da kima, domin kuwa dukiyar kasa za ta fita ne daga hannun mutanen nan masu halin gafiya, wacce ke diba ba don ta ci ba. Don haka muddin aka canza kudin kasar nan, to wadannan mutane sukan iya asarar dukiyar da suka kwasa ta mummunar hanya; in ya so mu da su kowa ma ya yi asarar tunda dama ai daga su sai ’ya’yansu ne.”

Canza kudin Najeriya kuskure ne – Isah Abdullahi

Hussaini Isah, a Jos

Alhaji Isah Abdullahi: ‘’A gaskiya kuskure ne a canza kudaden Najeriya, domin shi kansa Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ga illar canza kudi a lokacin da yake mulkin soja a kasar nan. A lokacin da dama al’ummar Najeriya sun yi matukar shan wahala, sakamakon canza kudin da aka yi. Don haka yanzu idan aka ce za a canza kudi, talakawan kasar nan ne za su sha wahala. Don haka bai dace ba kuma ba daidai ba ne a ce za a canza kudi a Najeriya. Canza kudi ba shi ne damuwar ’yan Najeriya ba a halin yanzu.
“Gwamnati ta san hanyoyin da za ta bi ta karbo kudaden da aka sace, don haka ta bi wadannan hanyoyi amma ba canjin kudi ba. Kuma wadannan mutane kusan dukkan kudaden da suke amfani da su, dala ne ba naira ba. Don haka canza kudi zai cuci talaka ne ba irin wadannan mutane ba.”

Ya kamata a canza kudin – Abdu Yerima

Sani Gazas Chinade

Alhaji Abdu Yerima mai shago: “A ganina, batun neman Gwamnatin Tarayya ta sake canza kudin kasar nan don tunanin wasu wadanda suka rike iko a kasar nan sun kwashi dukiyoyin jama’ar kasa ba ta hanyoyin da suka dace ba, in da za a yi hakan a gaskiya da an kyauta matuka. Dalilina na fadar hakan kuwa shi ne, ai kamar yadda aka taba yi ne a baya, can lokacin da tsohuwar Gwamnatin Janar Buhari ta soja ta canza kudin kasa; wanda hakan ya yi matukar tasiri, ta yadda wasu da yawa daga shugabannin wancan lokacin da suka kwashi dukiyoyin jama’ar kasa suka boye suka yi asarar dukiyoyin da suka tara. Don haka da yanzu ma za a yi hakan da an kyauta, kasancewar barnar da aka yi a yanzu ta fi ta baya can muni.”