Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu?

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]

Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu?
Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu?

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:

Tsarin bai dace ba – Sule Harka

Malam Sule Harka  da ke unguwar Surulere-Legas: “Bai kamata Gwamna ko Shugaban kasa ya jagoranci jam’iyya ba saboda yin haka zai shagaltar da su daga ayyukan da ya kamata su yi wa jama’a na ci gaba. Kuma idan ka duba, za ka ga ba su da lokaci. Kamata ya yi a ce wanda ba ya rike da wani mukami ya shugabanci ko ya jagoranci jam’iyya.”