Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 1

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]

Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 1
Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 1

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:

Tsarin ya dace – Muhammad Mai magani

Malam Muhammad Yahya Mai Magungunan Musulunci a Agege-Legas: “Ya kamata a ce Shugaban kasa ko Gwamna ya jagoranci jam’iyya, domin mutane sun fi ganin kimarsu kuma yin haka zai sa a sami tsari da bin doka da oda a cikin jam’iyyar fiye da a ce wanda ba ya rike da wani mukami ne yake jagorantar jam’iyyar.”