Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 2

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]

Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 2
Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 2

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:

Ba daidai ba ne haka – Lawal Maikifi

Malam Muhammadu Lawal Maikifi: “Jaorancin jam’iya, a ba zababbe ya zama rashin adalci. A ba shugaban jam’iyya cikaken iko a jam’iyya ya fi da a ba zababben. Shugaban jam’iyya shi ya fi kusa da talakawa tun daga mazabu har zuwa matakin tarayya kuma shi ne wanda ya yi yawo da dan takara har jama’a suka zabe shi. Haka kuma shi ya fi sanin matsalolin al’umma, don shi yake tare da su a ko’ina. Don haka shi ya fi dacewa ya zama sama da zababbe, don tabbatar da dimukuradiyya a Najeriya.”