Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 3
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:
Tsarin ne ya lalata dimukuradiyya – Adamu dahiru
Adamu dahiru Baba Ado: “Ai mayar da ikon jagorancin jam’iyyu hannun zababbun shugabanni shi ya kawo lalacewar siyasa a Najeriya. Idan ka dauko jamhuriya ta biyu, za ka ga ta fi tsari saboda jam’iyya ke sama da zababben shugaba. Idan zababben shugaba ya yi kuskure, to jam’iyya na da ikon ta ladabtar da shi kuma jam’iyya ke zaben wanda za a ba mukami don sanin irin wahalar da ya yi wa jam’iyya. Yanzu kuwa idan ka duba, zababben shugaba ke iko da kowa kuma ya kwashi kowa ya zuba a aljihunsa kuma shi ke ce wa jam’iya ga yadda za a yi. To ka ga shi ya haifar da lalacewar ci gaban dimukuradiyya a kasar nan.”