Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 4
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:
Shugaban jam’iyya ya dace ya fi iko – Sani Idris Jos
Alhaji Sani Idris Jos: “Shugaban jam’iyya shi ya kamata ya kasance jagora a harkokin gudanar da jam’iyyarsu ba shugaban gwamnatin jam’iyya mai mulki ba. Haka zai magance matsalar rarrabuwar kai a tsakanin magoya bayanta, saboda a duk lokacin da jagoran gwamnati ya zamo shi ne mai tabbatar da al’amura, to son zuciya da fifita na kusa da shi kawai zai yi barazanar hadewarta tare da kawo mata cikas wajen cin zabe.”