Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 5

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]

Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 5
Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 5

A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:

Tsarin bai kamata ba – Muhammad Ahmad

Muhammad Ahmad Tahir: “Shugaban jam’iyya shi ya kamata ya fi zama mai fada a ji a harkokin jam’iyya, shi ko jagoran gwamnati na kowa ne, har da mabiya jam’iyyun adawa ba na jam’iyyarsa kawai ba. Tsunduma kansa a harkokin jam’iyyarsu na iya dauke hankalinsa daga harkokin kasa tare da kawo masa bakin jini daga wajen wasu magoya bayan jam’iyyar da kuma al’ummar kasa gaba daya.”