Ko ya dace gwamnoni su jagoranci jam’iyyu a jihohinsu? 6
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da […]
A halin da ake ciki a siyasar Najeriya, Shugaban kasa shi ne jagoran jam’iyyarsa, a yayin da kuma a matakin jihohi, gwamnoni ne suka kasance jagorori. Wannan tsari tuni ya fara haifar da sabani da rikici a jam’iyyar APC. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace gwamnonin su kasance jagorori sama da shugabannin jam’iyyoyinsu a jihohi? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mabambantan jama’a, kamar haka:
Gaskiya bai dace ba – Bello Dallaji
Malam Bello Idris Dallaji dan tireda a Layin Charanchi Kaduna: “Gaskiya bai dace ba saboda idan aka bai wa gwamna jagorancin jam’iya sai wanda ya ga dama zai zama wani abu. Saboda abin da ke faruwa sai wanda gwamna ya ga dama zai zama Shugaban karamar Hukuma ko Kansila, koda kuwa ba a zabe su ba. Idan har gwamna yana yi da kai, za ka ci zabe koda kuwa takarar dan majalisa ka fito saboda haka sai wanda gwamna yake yi da shi za a yi da shi. Ko wani gwamna yana da karfi a jiharsa, komai adawarsa kuwa da fadar Shugaban kasa sai yadda ya ga dama zai yi a jiharsa muddin shi ne jagoran jam’iyya. Saboda haka a samu shugaban jam’iyya daban gwamna daban.”