Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?1

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya […]

Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?1
Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?1

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya nuna bukatar su yi haka. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace majalisun su sanya masa hannu? Ga ra’ayoyin ’yan Najeriya:

Kada su sake sa hannu – Sani Usman
Sani Usman: “Tun farko bai dace bangaren zartarwa ya mayar wa da majalisa wannan kundi ba saboda ya dauki lokaci da sanya hannu a kai. Me ya sa tun farko ba su dawo da shi ba sai yanzu? Wannan ya nuna cewa bangaren zartarwa ba su aikinsu yadda ya kamata. An ce tun watan Disamba aka tura shi amam ba a dawo da shi ba sai karshen watan Yuni, kin ga abin ya dau lokaci. Idan aka ce sai ’yan majalisa sun sake duba kundin, babu shakka za a sake daukar tsawon wani lokacin kafin ya zama doka. Haka kuma idan har suka sake duba kundin a yanzu, sun bayar da kofa nan gaba ma wasu su sake dawo da shi. Kin ga abin bai yi ma’ana ba.”

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50