Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?2
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya […]
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya nuna bukatar su yi haka. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace majalisun su sanya masa hannu? Ga ra’ayoyin ’yan Najeriya:
Bai kamata a sake sa hannu ba – Sarkin Ruwa
Sarkin Ruwan Ibadan, Alhaji Bala Ibrahim: “Ni ban amince ’yan majalisa su sanya hannu a kan kasafin kudin bana da Shugaba Jonathan ya sake aika musu ba. Da zarar suka sanya hannu, to kuwa sun bude kofar karuwar rashawa da sama-da-fadi da kudin jama’a, wanda Shugaban kasa yake so ya yi amfani da su ’yan majalisa wajen jawo hankalin al’ummar Najeriya, su amince su zabe shi a 2015 idan jam’iyarsa ta tsayar da shi takara.”