Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?4
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya […]
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya nuna bukatar su yi haka. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace majalisun su sanya masa hannu? Ga ra’ayoyin ’yan Najeriya:
Ya kamata su sanya masa hannu
– Aminu Mai Alayyahu
Malam Aminu Mai Alayyahu: “A nawa ra’ayi, lokaci ya yi da ’yan majalisarmu ya kamata su sa hannu cikin wannan kasafin kudi da Shugaban kasa ya sake gabatar musu, ko ba don komai ba, don a samu damar gudanar da ayyuka a kasar nan. Kodashike su ’yan majalisar suna da nasu dalilan na kin amincewa su sa masa hannu amma idan aka ci gaba da tafiya haka, ina tabbatar maka cewa ba za a samu damar gudanar da aiki ba. Kuma kamar yadda ka sani, talakawa ne hakan zai fi shafa ba su ’yan majalisar ko kuma Shugaban kasa ba.”