Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?6
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya […]
A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya nuna bukatar su yi haka. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace majalisun su sanya masa hannu? Ga ra’ayoyin ’yan Najeriya:
Ban goyi bayan su sake sanya hannu ba
– Ghali Sulaiman
Kwamared Ghali Sulaiman Kabiru: “Ni tambaya zan fara, saboda Allah ya aka yi Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi mantuwa irin wannan tun farko? Sai daga baya ya yi karin kudi a kasafin kudin bana, ai wannan abin kunya ne da ba mu taba ganin irinsa ba. Ya kamata ’yan majalisa su gaya masa cewa ya makara kuma kada su kuskura su sanya hannu a wannan kasafin kudi da ya sake aika musu, domin ana son yin amfani da karin kudin ne domin bayar da hanci da rashawa ga azzalumai masu yin zagon kasa ga kasar haihuwarsu.”