Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu […]
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
A rika bari mutane suna zabe da kansu – J. D. Hassan
Alhaji Jibrin danlami Hassan Bauchi: Bai dace wadanda ke kan sarauta su rika rantsar da ’ya’yansu kan gadon mulki ba, idan sun gaji ko tsufa ya tadda su. Ya kamata su bari talakawa su zabi wanda suke so idan lokacin yin hakan ya yi, wato in sun rasu ko kuma lokacinsu ya kare.
Abin bukata shi ne, kurum su tarbiyyantar da yaransu mulki da sanin darajar mutane shi ne ya fi alheri. Matukar suka zama sun dace su gaji mahaifansu idan sun rasu, talakawa da masu zabar sarkin za su zabe su don su maye gurbin mahaifinsu.
Amma idan suka sauka suka nada yaransu ko yaya halinsu yake to za su rika hada talakawansu da iyalan gidansu gaba, lamarin da zai iya sa idan sun rasun talakawa su yi wa yaransu bore ko kai musu hari da sunan ba sa kauna su mulke su, sai sun kawar da su daga karagar da mahaifan suka dora su”