Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?3
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu […]
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Su rika murabus tun suna raye ya dace – Salisu Mai Kananzir
Alhaji Salisu Adamu Mai Kananzir: “Ya dace sarakunan gargajiya su rika yin ritaya suna bar wa ’ya’yansu sarauta tun suna raye, domin bai dace ba a ce basarake ya yi tsufan da ba zai iya komai ba amma ya ci gaba da zama a kan mulki.
Yin haka cutarwa ce ga al’ummarsa da kasarsa ga baki daya. Don haka, ya dace idan har sarki ya ga ya fara tsufa, to ya sauka ya bai wa wani sarautar. Haka zai kawo ci gaba a masarautarsa kuma zai magance irin rikita-rikitar da ake samu wajen neman sarauta bayan rasuwar wani sarki.”