Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?4
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu […]
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Bai dace sarakuna su rika murabus ba
– Salisu Garba
Alhaji Salisu Garba Mai Suga: Shi mulki na Allah ne, Yana ba wanda Ya ga dama. Abin nema shi ne, koda hakan ta kasance, masu mulki suna so ’ya’yansu su gaje su, to su nemi yardar
Allah da ta talakawa, domin a zauna lafiya. Amma ba alheri ba ne a wayi gari mutum ya tura yaransa kasar Turai sun tashi da tarbiyya irin ta nasara, ba su san makamar mulki ko darajar mutanen kasarsu ta asali ba; rana daya don mahaifinsu ya ga ya tsufa, ya kira dansa ya dawo da shi ya dasa a kan mutane. Haka zai iya haddasa gaba da rashin zaman lafiya da kuma wargajewar kowace irin daula.
“Abin nema shi ne, a aiwatar bisa amincewar jama’ar da ake mulka don wanzuwar zaman lafiya kuma hakan shi ne zai sa wanda aka dora kan gadon mulki ya san darajar mutanensa da zai shugabanta.”