Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?5
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu […]
A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:
Ya dace su rika
murabus idan
sun tsufa
– Hamisu danmudi
Malam Hamisu danmudi: “Eh! To, gaskiya haka ya dace su rika sauka tun wuri, suna ba ’ya’yansu idan suka ga tsufa ya kama su; matukar dai yin hakan idan zai kawo ci gaba kuma mutane suna son wanda aka ba din. Sabod ai dansu na da ilimin zamani da na addini, za su kawo gagarumin ci gaba a masarautarsu. Idan zaben daya daga cikin ’ya’yan a ba shi sarauta ba zai zama matsala tsakaninsa da sauran ’yan uwa ba.”