Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram?
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Bai kamata a ciwo bashin ba – kasimu Aliyu
kasimu Aliyu, Sardaunan Matasan Assada: “A nawa ra’ayi, bai dace ba domin an dade ana yin ruwa kasa na shanyewa. Misali, an yi ta yi duk kasafin kudin da ake yi a kasar nan, akan ware kaso mafi tsoka ga harkar tsaro amma in ban da yunwa da fatara da ke addabar jami’an tsaro ba wani abu da dan Najeriya ya gani a kasa. A kan wannan na tabbata kashi 99 ba su goyon bayan wannnan harkalla, mu talakawan Najeriya ba mu goyi baya ba. Abin da kawai zai magance Boko Haram shi ne mulkin gaskiya da adalci da samar wa matasa harkar yi musamman na Arewa Maso Gabas da kawar da cin hanci da rashawa ba wai cin bashi ba. Da fatar Allah Ya kawar muna da wannan musibar, mu samu zaman lafiya a kasarmu ta gado.”