Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 1

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]

Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 1
Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 1

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Ban goyi bayan ciwo bashin nan ba – Alhaji Usman

Alhaji Usman Babangida, Kasuwar Malumfashi: “Ni dai kam ban goyi bayan cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya ciwo wannan bashi ba, domin kuwa Majalisar Tarayya bai kamata ta amince masa ya yi haka ba. Mu tuna da cewa ai an yi kasafin kudi na bana da ma na bara, inda aka rika ware wa harkar tsaro kimanin Naira tiriliyon daya, duk ina wadannan kudi suka shige? Na biyu, akwai al’amuran da suka dami al’ummar kasar nan suka kamata a maida hankali kansu, amma ba ciwo bashi domin Boko Haram ba. Mu duba matsalolin da suka hada da rashin aikin yi, talauci da rashin wadatattu kuma ingantattun hanyoyi da rashin wutar lantarki, duk wadannan sun sha gaban matsalar Boko Haram. Idan aka magance wadannan matsalolin, za a nemi Boko Haram a rasa. Idan kuwa Jonathan ya ce dole sai ya ciwo bashin nan, to zai kashe galarin gabansa ne kawai da kudin, tun da ga zabe nan ya karato.”