Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 2
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Babu cancanta a wannan bashin – Mansur Makama
Mansur Makama: “Ra’ayina game da wannan zurmugudu da ake son yi mana, to ko ba komai na san babu cancanta a cin wannan bashin. Duk kudin da aka kashe kan tsaro amma lamarin bai canja ba, wannan shi ke nuna suna amfani da tsaro ne kawai suna cin kudinsu. Ko bashin suka amso talakawa ba za su san yadda kudin za su bace ba, kansu ne za su ranto wa kudin ba kasa ba. Ga shi ana fuskantar zabe nan da wasu watanni masu zuwa. Wadanda suka kasa kawo wa kasa ci gaba ta fuskar ilmi da tattalin arziki da lafiya, kullum matsalar tsaro bunkasa take yi kuma kawai domin mun koma jakuna a ce za a ranci kudi don magance mana matsalar tsaro? In har kudin da muke da su a kasar nan sun gagari magance matsalar, to kuwa bashi ba zai iya sanya mata ruwa ba, don haka a fito mana da wata hanya ba wannan ba, kifi na ganinka mai jar koma.”