Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 3

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]

Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 3
Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 3

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Babu wani alfanu ga bashin – Umar Gwarmai

Alhaji Umar Gwarmai, Unguwar Sabo Ibadan: “A gaskiya ban ga amfanin karbar bashin kudi masu yawa irin wannan ba, domin magance matsalar Boko Haram. Kudin da Shugaba Goodluck Jonathan yake cewa zai karbo na Dala miliyan dubu daya, sun yi yawa kwarai da gaske. Akwai alamar cewa Gwamnatin Tarayya tana son ta yi amfani da wadannan kudade ne wajen biyan bukatun siyasa domin yin amfani da kudi wajen sayan kuri’un jama’a da danne musu hakki a zaben 2015, a maimakon kyautata tsaron lafiyar jama’a. Da yawa mutane ba su fahimci manufar Shugaba Jonathan ba, amma mu dai mun gano gaskiyar nufinsa na yin amfani da kudi wajen sake darewa kujerar shugabancin kasa ce.”