Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 4

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]

Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 4
Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 4

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Lallai cin bashin bai dace ba – Mansur Inuwa

Mansur A. Inuwa Unguwar Sabo Ibadan: “Ina ganin bai dace ba ko kadan a karbo bashin irin wadannan makudan kudi a kan batun Boko Haram. Su da kansu shugabannin kasar nan suna sane da hanyar da za su iya yin maganin matsalar Boko Haram ba tare da karbo bashin kudin ba. Irin wannan bashin kudi yana kara durkusar da talakawa da ci gaban kasa ne. Ya kamata shugabanni su ji tsoron Allah, domin idan ba sa ganin Allah to, Shi yana ganin irin kwabasuwar da suke yi da wasoson dukiyar jama’a wanda Allah (TWT) ba zai kyale su ba. Tun a nan duniya za su fara girbar irin abubuwan da suka shuka kafin mu koma gaban Allah da babu lauyan kariya sai gaskiya tsantsa.”