Ko ya dace Shugaba Jonathan ya ciwo bashin Naira bilyan 168 don yaki da Boko Haram? 5
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma […]
A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya tura wa Majalisar Tarayya bukatar su amince masa ya ciwo bashin Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 168), domin yaki da Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a ciwo wannan bashi, a wannan lokaci? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Bai kamata a ciwo bashin ba – Zayyana Mamman
Zayyana Mamman Mai Walda, Malumfashi: “Ni dai a ra’ayina, maganar Boko Haram ba tabbas ba ce, domin kuwa akwai abubuwa masu muhimmanci da ya kamata a tunkara a magance su, maimakon Boko Haram. A halin da ake ciki, al’amuran kasa sun tabarbare, kamata ya yi a tunkari aikin samar da ingantattar wutar lantarki, a kula da sashin lafiya, domin samar da magunguna da kwararrun likitoci, a samar da kafafen ayyukan yi, yadda matasa za su samu aikin yi, a magance zaman banza. Idan aka yi haka, matsalar Boko Haram da kanta za ta kau, domin kuwa kamar yadda na fada, harkar Boko Haram ba ta da tabbas. Don haka, lallai ne a dakatar da batun ciwo bashin nan, a tunkari harkar gina kasa kawai da al’ummarta.”