Ko ya dace shugabanni su bayyana kadarorinsu a bainar jama’a?

Kamar yadda tsarin mulki ya tanada, duk wani mai rike da mukami, tun daga Shugaban kasa, Gwamnoni, Ministoci da sauransu, za su bayyana kaddarorin da suka mallaka ga hukuma kafin da bayan kammala mulkinsu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace su rika bayyana kaddarorin nasu a bainar jama’a ko kuwa a sirri? […]

Ko ya dace shugabanni su bayyana kadarorinsu a bainar jama’a?
Ko ya dace shugabanni su bayyana kadarorinsu a bainar jama’a?

Kamar yadda tsarin mulki ya tanada, duk wani mai rike da mukami, tun daga Shugaban kasa, Gwamnoni, Ministoci da sauransu, za su bayyana kaddarorin da suka mallaka ga hukuma kafin da bayan kammala mulkinsu. Abin tambaya a nan shi ne, shin ya dace su rika bayyana kaddarorin nasu a bainar jama’a ko kuwa a sirri? Wakilanmu sun tuntubi jama’a kuma ga abin da suke cewa:

Su bayyana a fili ya fi – Masa’udu Umaru

John D. Wada, a Lafiya

Alhaji Masa’udu Umaru: “Ni a nawa ra’ayi, ba laifi ba ne wadannan sababbbin ’yan siyasa da aka zaba su bayyana dukiyoyinsu ga jama’a kafin su kama aiki. Domin muna mulkin dimokuradiyya ne. Da muna mulkin soja ne za su iya bayyana kadarorinsu cikin siri. Amma tunda muna dimokuradiyya ne haka zai ba jama’a damar tantancewa bayan ’yan siyasan sun kammala wa’adinsu, su gane ko sun ci kudin jama’a ko ba su ci ba. Hakan kuma ba shakka zai taimaka wa su kansu ’yan siyasar. Domin idan ba su ci kudi ba za a gane kuma babu wanda zai zarge su.”

Su bayyana kowa ya sani – Isa Moyi

John D. Wada, a Lafiya

Alhaji Isah Moyi: “Ba shakka ya da ce ’yan siyasa su rika bayyana kadarorinsu kafin su fara aiki. Don da yawa ba a iya ganewa idan suka saci kudin jama’a, domin ba su bayyana kadarorinsu ba kafin suka fara aiki. Don haka tun da ba wai za a kwace dukiyarsu ba ne, ya kamata su rika bayyanawa kafin su fara aiki. Ka ga ta haka ne talaka zai sani ko an danne masa hakki ko ba a yi ba.”

Ya dace a su tantace a fili – Dauda Hamisu

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Dauda Hamisu: “A ra’ayina, ya dace a yi irin wannan bincike a bayyane musamman da yake jama’a ne domin ra’ayin kansu suka zabi wadannan shugabanni, domin su yi musu ayyukan ci gaban rayuwarsu. Ana iya samun matsalolin son zuciya da karya da cin hanci idan aka yi binciken cikin sirri. Amma idan aka yi binciken a bayyane to, mu talakawa da muka zabe su za mu fahimci cewa, sun fara sauke wani nauyi da suka dauka. Yin haka zai taimaka mana wajen gano gaskiyar wadannan zababbun mutane ta yadda za mu iya sake zabarsu bisa mukaman da suke so a zabukan gaba idan suka sake fitowa. Duk wanda ya nuna karya da son zuciya daga cikinsu, ya kasa cika mana alkawari, sai mu kauce masa domin mun fahimci ba mutumin kirki ba ne.”

Na goyi bayan su bayyana – danlami Umar

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Alhaji danlami Umar Muhammad: “A gaskiya ya kamata a yi binciken a bayyane domin amanar jama’a ce aka damka a hannunsu kuma ya kamata wadannan jama’a da suka zabe su bisa sababbin mukaman su waye da komai kafin su fara aiki. Ai a bayyane wasu ’yan majalisu na jihohi da na tarayya da gwamnoni suka rika wawason dukiyar jama’a ba kan gado. To mene ne laifi idan a yanzu an binciki dukiya da kadarorinsu a bayyane domin dakile aukuwar irin wannan barna a gaba? Su ma ’yan majalisu na jihohi da tarayya da gwamnoni da suka sha kaye ko suke barin gado, ya dace a yi musu irin wannan bincike domin zai hana baragurbi daga cikinsu yunkurin sake dawowa neman wani mukami a nan gaba.”

Hakan zai rage almundahana – Zubairu Sham’una

Muhammad Yaba, a Kaduna

Zubairu Shan’una: “Ya dace su bayyana kadarorin da suka mallaka, domin zai rage cin hanci da rashawa a kasa. Idan ya zama doka cewa duk wani dan siyasa da aka zaba ya bayyana dukiyarsa wannan zai kawo karshen yawan rikice-rikice da ake yi wajen neman kujerun siyasa. Amma saboda rashin yin hakan ne ke janyo ribibi lokacin yakin neman zabe har take kai wa ake fada wajen neman zabe.”

Hakan zai taimaka wajen tantancewa – dahiru Ahmad

Muhammad Yaba, a Kaduna

dahiru Ahmed: “Bayyana kadarorin masu rike da mukamin siyasa zai taimaka wajen gane nawa mutum ya mallaka kafin hawansa mulki da kuma bayan ya sauka. Kuma yin haka zai taimaka matuka wajen gudanar da gwamnati a bude ko a bayyane. Domin rashin bayyana kadarorin ne ke janyo rashin gaskiya da rikon amana a gwamnatance.”