Ko ya dace ’Yan Majalisun Tarayya su yi wa kansu dokar samun fansho har iya rayuwarsu?
A kwanakin baya ne aka fara batun cewa Sanatoci da ’Yan Majalisar Tarayya suna yunkurin tattauna batun samar da dokar da za ta ba su damar sama wa kansu fansho, wanda za a rika biyan su har tsawon rayuwarsu, kamar dai yadda ma’aikatan gwamnati ke samu bayan sun kammala aiki. Abin tambaya a nan shi […]
A kwanakin baya ne aka fara batun cewa Sanatoci da ’Yan Majalisar Tarayya suna yunkurin tattauna batun samar da dokar da za ta ba su damar sama wa kansu fansho, wanda za a rika biyan su har tsawon rayuwarsu, kamar dai yadda ma’aikatan gwamnati ke samu bayan sun kammala aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace su gabatar da wannan doka ko kuwa? Wakilanmu sun gana da mutane daban-daban, kuma ga ra’ayoyinsu:
Wannan bai dace ba – Abdullahi Sani
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Alhaji Abdullahi Sani Imam Shagamu: “A gaskiya bai dace ’yan majalisu su yi wannan doka ba, domin kuwa yin haka zalunci ne. Idan muka lura, ni dai ban taba jin wata kasa a duniyar nan an taba yin haka ba, kuma sai yanzu a ce a Najeriya za a yi haka? Don haka ina kira ga ’yan majalisun da su yi wa kansu kiyamul laili tun da wuri, domin bai kamata su yi wannan dokar ba. Kuma ya kamata su tuna da cewa, kafin a zabe su, sun yi wa mutane alkawurra daban-daban. Don haka su maida hankali wajen cika alkawuran da suka dauka, ba wai su aiwatar da wani abu na biyan bukatun kansu ba, domin kuwa wannan zalunci ne ga talakawa.”
Ban goyi bayan yin dokar ba – Usman Babangida
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
Alhaji Usman Babangida Malumfashi: “Wannan batu na fansho ga ’yan majalisu gaskiya bai dace ba, domin idan suka yi haka, to ba su yi abin da ya kai su majalisun ba. Idan sun mance, ya kamata su tuna cewa sun je majalisun ne domin su wakilci talakawa, domin su kawo abin da zai kawo jin dadin rayuwar talaka amma ba domin dadad wa kansu su kadai ba. Saboda haka, bai kamata su hada kansu da ma’aikatan gwamnati ba, wadanda ke kwashe shekaru 35 suna aiki wa al’umma ba. Su sani cewa su tsawon lokacinsu fa shekaru hudu ne kacal, don haka saboda me za a ba su kudin fansho har tsawon rayuwarsu? Gaskiya wannan ba daidai ba ne, don haka su sake dubara.”
kudurin dokar nan bai dace ba – Sama’ila Rogo
Abbas Ɗalibi, a Legas
Malam Sama’ila Rogo: “Yin wannan ƙudiri bai dace ba, domin idan su sun yi haka na gabansu ma sun yi, to shi talaka mai za a bar masa? Wannan aniya tasu ta bayyana mana cewa su ba kishin ƙasa ne a gabansu ba, ba su tausayin talaka, kansu kawai suka sani. Don haka ba su damuwa da abin da ya shafi jama’a sai na kawunansu kawai.”
Wannan dokar ta hadama ce – Salisu Bashankai
Abbas ɗalibi, a Abekuta
Alhaji Salisu Bashankai: “A gaskiya bai dace ba Sanatoci da ’Yan Majalisun Tarayya su ƙiƙirar wa kansu fansho na har tsawon rayuwarsu, domin su zaɓen su aka yi na wasu ƙayadaddun lokaci kuma ana biyan su dukkanin haƙƙoƙinsu; don haka wannan ƙuduri da suka sanya a gaba ya daɗa fito da haɗamar su a fili tare da babakeren su a kan dukiyar talaka.”
Wannan rashin adalci ne – Habiba Musa
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Habiba Musa Aminu: “Ko kadan, sam bai dace ba a yi haka, yin hakan rashin adalci ne. Bai dace ba, domin wasunsu tsofaffin ’yan fansho ne kuma alawas din da dayansu ke dauka a wata ya fi yawan albashin wanda ya shekara 35 yana aikin gwamnati a mtsayin darekta; tun daga farkon shigar sa har ya zuwa lokacin da ya yi ritaya. Kuma su ai shekara hudu rak suke yi, wasu kuma su karbe su, to idan aka ce za a biya su to lallai za a maida siyasa bankin da ya fi kowace sana’a ko aiki samun kudin shiga, don haka kowa ya kamata ya bar abin da yake yi, don ya zama dan majalisa; don shi ma ya zama dan fansho da garatuti. Kukan kurciya jawabi ne.”
Babu adalci a nan – Adamu Nuhu
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Adamu Nuhu ’Yan Kwada: “Idan an ba su fansho da garatuti, mu kuma masu zabe a ba mu nawa? Biyan ’yan majalisu wani alawas ma bayan kammala shekara hudu rashin adalci ne. Da a yi haka gara a cika alkwarin da Baba Buhari shugaba ya yi; na biyan matasa da dattawa marasa galihu tallafin Naira dubu biyar, wanda su ’yan majalisun suka soke lokacin da aka gabatar a gabansu. Shi ma talakan da ya zabe su, sai ya karbi nasa garatutin da fansho ko? Maimakon a ba su su kadai.”