Ko ya dace ’yan takarar siyasa su rika tirjiya idan sun fadi zabe?
Yana nema ya zama kamar halayya ga ’yan siyasa a Najeriya, idan suka fadi zabe sai su ki amincewa da an kada su. Wadansu su yi ta korafi, wadansu su tafi kotu, a yayin da wadansu ma kan karya doka wajen shirya tashin hankali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace ’yan siyasa […]
Yana nema ya zama kamar halayya ga ’yan siyasa a Najeriya, idan suka fadi zabe sai su ki amincewa da an kada su. Wadansu su yi ta korafi, wadansu su tafi kotu, a yayin da wadansu ma kan karya doka wajen shirya tashin hankali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace ’yan siyasa su rika yin haka? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban dangane da haka kuma ga abin da suke cewa:
Rashin yarda da kaddara ce– Auwal Usman
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Auwal Usman Goni: Ra’ayina shi ne, rashin yarda da kaddara ce ke sa dan takara ba ya amincewa da shan kaye da wuri. Da dan takara zai yarda da kaddara kamar yadda dan takarar Gwamnan PDP na Gombe Sanata Bayero Nafada ya yi, cewa ya yarda da kaddara kuma ba zai je kotu ba, da ya fi musu. Kaddara ita ce yarda da abu mai kyau da marar kyau kuma da ma dan siyasa ya kamata ya san akwai ci akwai faduwa.
Wannan lalata dimokuradiyya ce – Umar Zubairu
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Umar Zubairu: A gaskiya irin abin da wadansu ’yan takarar mukamai da suke yi na kin amincewa da kayen da aka yi musu bayan samun sakamakon zabe suna yin haka ne domin ra’ayin kansu kuma ina ganin suna yin haka ne domin hargitsa zaben gaba daya da zai haifar da koma baya da ci gaban al’ummarsu. Hakan bai dace da salon siyasar dimokuradiyya ba, domin su kansu sun san cewa sun sha kaye kuma ba su da dalilin jn kafa. Duk mai hankali zai iya fahimtar bayanan da irin wadannan mutane suke yi bayan sun fadi a zabe, suna yi ne domin haifar da rikicin siyasa. Idan har suna daukar irin wannan mataki suna nufin ba sa kaunar ci gaban jama’arsu, kuma jama’ar tasu za ta yanke hukuncin ci gaba da goyon bayansu ko akasin haka a nan gaba.
Na kusa da ’yan takara ne ke hana su yarda – Zainab Shehu
Daga Rabilu Abubakar, Gombe
Zainab Shehu: Ra’ayina shi ne, mutanen da ke kusa da ’yan takara ne suke hana su yarda da rungumar kaddara a kan lokaci. Mutanen da ke wakilta ne a lokacin zabe, su ne suke zuwa INEC su yi zuga, su kuma sai su yarda a kan hakan zugar da suke yi su ce kada ka yarda da faduwa, kai ka ci zabe aka yi maka magudi kuma za a je kotu. Wadanda suka fi yin haka su ne wadanda ya wakilta zuwa INEC din saboda su ne suka san abin da ya wakana. Don haka abin da suke yi bai dace ba, ya kamata su rika daukar kaddara, su amince sun fadi zabe kawai cikin lumana.
Kamata ya yi su rika hakuri – Abdullahi Bako
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Abdullahi Bako: Ina ganin idan mutum ya fadi zabe kamata ya yi ya bar komai ga Allah, maimakon ya rika bin wasu hanyoyi na ganin sai lallai ya samu mulki ta karfi ko sai an tursasa mutane sun zabe shi da sauransu. Ya kamata mutane su fahimci cewa Allah ne ke bayar da mulki.
Wannan dabi’a ba ta dace ba – Musa Abubakar
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Musa Abubakar: Rashin rungumar kaddara ce ta haifar da wannan dabi’a mara kyau da wadansu ’yan siyasa masu neman mukamai suka dade suna yi a Najeriya. Kamata ya yi idan har sun tabbatar da gaskiyar sakamakon zabe, to su yi abin da siyasa ta gada na yin nasara da fadowa tare rungumar kaddara zuwa wani lokaci a gaba. Ina ganin irin wannan dabi’a da suke dauka ta kin amincewa da faduwa a zabe tana da mummunar illa ga tabbatar dimokuradiyya a Najeriya, domin hali ne mara kyau da suke koya wa na baya. Ya kamata nan take su rika fitowa suna nuna farin ciki tare da taya abokin takararsu murna a lokacin da suka ji sakamakon shan kaye maimakon korafin da ba ya da amfani gare su da kasar haihuwarsu.
Wannan hali bai dace ba – Murtala Abdurrahman
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Murtala Abdulrahman: A ra’ayina, idan har aka bayyana cewa mutum ya fadi zabe to ya karbi kaddara, idan har ya ga ba zai hakura ba, to akwai kotu sai ya je ya nemi hakkinsa a can; ba tare da ya bi wasu hanyoyi na ganin cewa an soke zabe ba.