Ko ya dade a ba ‘yan Majalisu kariya kamar yadda doka ta ba Shugaban kasa da Gwamnoni?
A ‘yan kwanakin nan ne wasu daga dikin ‘yan Majalisa suka tayar da batun neman a ba su kariya kamar yadda Shugaban kasa da gwamnoni suke da kariya. Lamarin ya janyo dede-kude a tsakanin al’umma, inda mutane k e ta tofa albarkadin bakinsu a game da batun. Hakan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya […]
A ‘yan kwanakin nan ne wasu daga dikin ‘yan Majalisa suka tayar da batun neman a ba su kariya kamar yadda Shugaban kasa da gwamnoni suke da kariya. Lamarin ya janyo dede-kude a tsakanin al’umma, inda mutane k e ta tofa albarkadin bakinsu a game da batun. Hakan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane, kuma ga amsar da suke bayarwa:
Bai dade a ba ‘yan majalisa rigar kariya ba – Murtala Lawal
Daga Ahmed Ali, Kafandhan
Murtala Lawal: Maganar gaskiya bai dade a bai wa ’yan majalisunmu wata kariya ba. Ina ganin ga duk wani mai son ganin di gaban kasar nan da samun jagorandi na gari ba zai goyi bayan ba ’yan majalisa kariya ba.
Ni ba ma ’yan majalisa ba, hatta sauran masu rigar kariyar ma daga shugaban kasa zuwa gwamnoni bai kamata ya zama suna da rigar kariya ba. Domin wannan kariyar de ta gurbata mana kasa shugabanni su ka yi ta barnata dukiyar kasa kamar ba gobe yanzu ga halin da mu ka tsindi kanmu kowa na ji a jikinsa.
Abinda zai haifar da adaldi da di gaba kawai shine duk wani xan kasa da aka samu da aikata laifi tun daga kan shuwagabanni har zuwa talakawa ko waye mutum a hukunta shi kawai wannan shi zai sa masu aikatawa su kiyayi kan su su kuma masu shirin yi su yiwa kansu kiyamullaili ka ga hakan shi zai sa kasa ta gyaru.
Bai dade a ba su kariya ba
– Kabir A. Abasaya
Daga Ahmed Kabir S/kuka a Katsina
Kabir A. Abasaya: Dalilina na rashin ganin dadewar bai wa ‘yan majalisa kariya irinta Gwamna ko Shugaban kasa shi ne idan har suka samu wannan damar to za su rika yin abin da suka ga dama diki kuwa har da din mutundin jama’a, karya doka da gangan tare da duk wasu abubuwa marassa daxi ga al’umma ba wai ga abokan adawar siyasarsu ba kaxai, domin takamar suna da wannan kariya. A yanzu ma da basu da ita yaya suke gudanar da abubuwansu? to ina ga ande ga wata kariyar da za ta hana a gurfanar da su a gaban kotu?
Bai kamata ba – Abdulazeez M. Turaki
Isiyaku Muhammed
Abdulazeez M. Turaki: Gaskiya a nawa ra’ayin bai kamata a ba ’yan majalisa ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya ba shugaban kasa. Saboda maganar gaskiya ita de tsammankin da ke kan shugaban kasa da gwamnoni bay a kan ’yan majalisu. Kuma za su iya amfani da kariyar wajen dutar da shugaban kasa da hana shi yin abun day a kamata.
Yana da kyau a ba su kariya
amma – Abdulmutallab Tijjani Tahir
Daga Ahmed Ali, Kafandhan
Abdulmudallab Tijjani Tahir: Ra’ayina shi ne da ‘yan majalisa za su gyara tsarinsu da mu’amalarsu a matsayinsu na shugabanni, sannan su kiyaye da hakki da muradun jama’ar yankinsu, ban ga laifi ba idan an basu kariya sai dai matsalar kawai guda xaya de kusan Najeriya daga talakawan har zuwa shugabannin suna bukatar daidaita sahu tukuna domin maganar gaskiya yawandi an riga an gurbade. Idan ka lura ba wai matsalar basu kariyar ne abin gudu ba amma a yanzun ma da babu kariyar yaya alakarsu take da talakawansu? Ina de kowa na yin abinda ya ga dama ne kuma ba tare da tsoron komai ba? Ya kamata a duba a gani shin basu kariyar zai amfanar da kasar ne ko ko xaixaikunsu kawai zai amfanar don dimma wasu muradunsu na kashin kai! To da ade komai ya gyaru ne tsaf-tsaf, ban ga laifin basu kariya ba. Yawandi dama ana tsoron bada kariya ne saboda rashin yarda da amindi tsakanin waxanda suka damka musu amanar da waxanda aka basu amanar.
Basu dandanta ba
–Alhaji Alah M. Katsina
Daga Ahmed Kabir S/kuka a Katsina
Alhaji Alah M. Katsina: Ga yanayi irin na xan siyasar Najeriya wanda shi kullum kanshi kawai ya sani, to irin wannan kariya ta tsaya kan waxannan mutane biyu kawai, wato Shugaban kasa da Gwamna. Amma maganar ade wai xan majalisa ya samu irin wannan kariyar ai an shiga uku. Mu dubi fa irin yadda suke yi wa dokokin kasar nan karan tsaye, ko suke yin amfani da matsayar kujerunsa na yin duk wani abin da suke so ba tare da lura da irin matsayinsu ba, kuma suna sane da batun kotuna wanda har wasu lokutan kotu za ta neme su amma sai sunga dama su je. To yau sai aka de suna da wata kariyar da ba za a kama su har kuma su gurfana a gaban kotu ba. Mun ga dai abin da ya faru a baya da kuma waxanda suke faruwa a yanzu ga su waxannan ’yan majalisa. Saboda haka ni banga dadewar a ba su wannan kariya ba.
Ban goyi bayan haka ba – Bello Sagir
Isiyaku Muhammed
Bello Sagir: Bana goyon bayan ayi doka da za ta bai wa ’yan majalisu rigar kariya, domin ni a gani na, ai daman tuntuni suna da kariya a tare da su. Misali, ana zabar mutum, ko kuma yana yin maguxin zabe, majalisa yake guduwa ya labe. Ba a kara ganin yawandin su sai an kaxa gangan siyasa. In kuma ma an kai kararsu sai lauyoyin su su yi sauri su je su kare su. A wasu lokutan ma sukan saye alkalan domin samun nasara a shari’ar. Wannan ja’irar doka ta kariya fa da gwamnoni da shugaban kasa ma ke amfana da ita ma ta saba wa tsarin mulki na 1999 sixira ta (1) sashe na (1). Duk da dewa kuma sashe na (308) ya basu kariyar. Amma shi fa na sashe na (1) sashe ne na sahun giwa mai take duk wani sashe da yadi karo da shi, saboda haka ya take sashe na (308) xin ya murkushe shi, saboda ya di karo da shi, a mahangar doka!
Yawandin ’yan majalisa musamman na dattijai, tsofaffin gwamnoni ne, saboda haka yanzu idan aka yarda suka bai wa kansu kariyar, zai kasande mutum zai fita daga kariya ta gwamna ya shiga kariya ta majalisa, saboda haka a majalisama sai ya yi ta maimaita wa har ya mutu a dan. Ke nan duk badakalar da ya yi ba a da yadda za ayi da shi saboda kawai rigar kariya. Kariya ga ’yan majalisa zai kara nunnunka kuxin da ake kashewa domin yin takarar, wanda hakan kuma kwata-kwata ba alheri ba ne ba.