Ko ya kamata a ci gaba da nemo danyen Mai a yankin Arewa maso Gabas?

A dakatar da wannan aiki – Mista Omowale Akinbowale Daga Abbas Ɗalibi, a Abeokuta Mista Omowale Akinbowale: A ra’ayi na, Najeriya ta janye hannunta kacokan game da wannan aikin na haƙar man fetur  a wannan yankin, domin tun da fari ma an aza harsashin aikin ne bisa dalilai na siyasa, da za ka ji irin […]

Ko ya kamata a ci gaba da nemo danyen Mai a yankin Arewa maso Gabas?

A dakatar da wannan aiki – Mista Omowale Akinbowale

Daga Abbas Ɗalibi, a Abeokuta

Mista Omowale Akinbowale: A ra’ayi na, Najeriya ta janye hannunta kacokan game da wannan aikin na haƙar man fetur  a wannan yankin, domin tun da fari ma an aza harsashin aikin ne bisa dalilai na siyasa, da za ka ji irin maƙudan kuɗin da aka salwantar a aikin za ka san da walakin Goro a miya, sai gashi kuma yanzu aikin na cin karo da matsalar tsaro a yankin abin da ya zamo barazana ga rayukan ƙwararu da masana da ke aikin dama ƙarin asara da ƙasar ke tafkawa a kullum a kan aikin,  don haka ni a ra’ayi na dakatar da aikin shi ne ya fi zamo wa ƙasar nan alheri, wajibi ne ƙasar nan ta dinga bin shawarwarin masana a wannan aiki da ta ɗauko.

Bai kamata a dakatar ba – Mamman Goma

Daga Isiyaku Muhammed

 

Mamman Goma: Gaskiya bana goyon bayan dakatar da nemo danyen mai a yankin Arewa maso Gabas, domin wannan ba karamin ci gaba bane gare mu ‘yan Arewa. Abin da ya kamata ayi kawai shi ne a samar da matakan tsaro domin kiyaye masu wannan aiki har a samu nasara.

Bai kamata a dakata ba – Alhaji Musa Shabiri

Daga Abbas Ɗalibi, a Legas

 

Alhaji Musa Shabiri: Ra’ayina a kan aikin  haƙƙar mai da ake yi a Jihar Barno a Arewa bai kamata a dakatar da wannan aiki ba, domin wasu ne ke son yi wa wannan aiki ƙafar angulu, domin sun ga an kusa cinmma manufar, don haka saboda wata buƙata tasu suke son su daƙile ci gaban ‘yan Arewa, don haka ko kaɗan kada gwamnati ta saurara a kan wannan aiki na ci gaban ƙasa, kamata ya yi a samar da ƙwararan matakan tsaro a wannan wajen domin bai wa masu wannan aiki tsaro don su samu ƙwarin gwiwar ci gaba da aikin.

Ya kamata a ci gaba – Hussaini Hammangabdo

Daga Amina Abdullahi, Yola

 

Hussaini Hammangabdo: Eh, ya kamata a ci gaba da nemo danyen mai domin alheri ne a Najeriya, kuma in aka yi nasara aka samu wannan man, babu shakka zai samar wa jama’a aikin yi musamman matasa.

Abu na biyu shi ne, matsalolin da ake samu na tsageru a can kudancin Najeriya, yadda suke ganin kamar su suke rike da arzikin kasar, wannan zai kau da hakan. Sannan kuma wannan ci gaba ne sosai. Ya kamata a ci gaba sannan a jajirce ta gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha da kuma arewa maso gabas, a hadu karfi da karfe domin tabbatar da nasarar samin wannan abu.

Dukiyoyin Najeriya gaba daya ta sakamakon wannan man ne aka same ta. Ashe in aka samu Arewa maso Gabas lallai kudin shigan Najeriya zai karu. Koda yake akwai kalubale da ake samu kamar na rashin tsaro da sauransu, ko a gidanka ne kake kana da kalubale. Don haka kar wannan ya tsoratar da jama’a ko gwamnati domin jami’an tsaro na iya kokarinsu don ganin sun samo tsaro wannan babban nasara ce.

Ina goyon bayan a ci gaba – Usman Muhammad

Daga Amina Abdullahi, Yola

 

Usman Muhammad: Eh, domin abin da ya dace ayi kenan, amma ko an ci gaba da hakan mai, ya kamata a ce duk bangarori na tattalin arziki suma a taba su kar a yi kuskuren da aka yi na farko, daga samun mai sai aka manta da su noma da sauran al’amura wadda sune tushen arziki. Kamar yadda bahaushe ke cewa noma shi ne tushen arziki.

Wannan arziki ne na zamani sannan a gaskiya ya kamata ko saboda gorin da ake mana a Kudanci wai su suke da arziki. Suna ganin cewa mai dinnan shi ne arziki. Gaskiya arziki ne amma idan aka taba wannan bangaren, ya kamata sauran bangarorin ma a tabasu. Domin muna da ma’adinai wadanda suka fi mai daraja.

Matsalar shi ne kudin da za a kashe wajen gano man. Sannan kuma idan aka gano man, a fara aiki gadan-gadan.

Domin idan ana yi ana tsayawa, sai wats gwamnatin ta zo ta yi watsi da shi. Koda yake yana  daukar lokaci kuma yana cin kudi, anma da ruwan ciki ake debo na rijiya.

A ci gaba da aiki – Abubakar Majidadi

Daga Isiyaku Muhammed

 

Abubakar Majidadi: A ci gaba da aiki kawai. Ai burin Boko Haram ke nan da sauran dukkan kungiyoyin ‘yan ta’adda. Idan aka tsayar da aiki, za su yi murna ganin cewa har sun isa su hana ci gaban kasa. Wannan aikin nemo man yana da matukar muhimmanci ga Arewa. Idan muka samu mai, ba wani dan Kudu da zai kara daga mana yatsa. Don haka a tura sojoji wajen aikin, sannan a ci gaba da aiki, kuma da yardarm Allah za a samu nasara.