Ko ’yan Najeriya za su bai wa Atiku dama?

Najeriya kasa ce da ke bukatar gwarzon shugaba, hadaddiyar kasa da ke bukatar adalin shugaba da zai kawo karshen kashe-kashen da ake babu gaira babu dalili, kasar dake neman mutumin da zai sadaukar da kai da samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa da ke garari a tituna ko zaman kashewando. Wannan kasar na da […]

Ko ’yan Najeriya za su bai wa Atiku dama?
Ko ’yan Najeriya za su bai wa Atiku dama?

Najeriya kasa ce da ke bukatar gwarzon shugaba, hadaddiyar kasa da ke bukatar adalin shugaba da zai kawo karshen kashe-kashen da ake babu gaira babu dalili, kasar dake neman mutumin da zai sadaukar da kai da samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa da ke garari a tituna ko zaman kashewando.

Wannan kasar na da bukatar mutumin da ba shi da tsoro ko shakka, kuma mai hange akan yana yin kowa wanda in yace Ee to haka yake, in kuma ya ce a’a. Tofa maganarsa dutse ne, Najeriya tana neman mutumin da zai samar da mafi akan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
kasar Najeriyan a bukatar mutumin da ke da dimbin basirar da zai iya gano inda aka gaza da kuma nasarar da aka samu tare da fahimtar ina ya kamata a gyara da na ci gaba, ba ma son gaula, ko lusarin shugaba da zai zama tamkar dan amshin shata.
Amma alamu sun nuna Atiku AbubakarTuraki Adamawa kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya daga 1999 zuwa 2007, shi ne kadai zai iya cimma nasarar wannan bukatar ba tare da ance wayyo Allah ba, saboda basirar da yake da ita ta shekaru takwas ya san ciki da wajen matsalolin kasar, kuma zai magancesu.
Muna bukatar mai farin jinin da ke da abokai ko mutanen kwarai a ciki da wajen Najeriya, Atiku Abubakar ya yi cudanya da muhimman mutane a cikin kasar nan, kamar a Lagos akwai Bola Ahmed Tinibu, a Katsina, Kaduna, Kano, akwai irinsu Malam Garba Shehu da Musa Ilaila da Ajigawa Mutawalle Hadeja, a Ribas, Prince Tony, Prince Will, a Ebony, Cif Cukwu Emeka Eze, a Anambra Farfesa Charles Cukwuma Soludo na tuna muna zaune a jirgin sama kusa da kusa, ya tambayeni wata jarida da nake karantawa bayan mun sauka a Katsina, sai na tamabaye shi ko me ya sa yake goyon bayan Atiku Abubakar da ya zama shugaban kasa? Sai ya ce ai Turaki Adamawa jan gwarzo ne da zai iya farfado da martabar tattalin arzikin kasar nan, ban da ba tabbatar dacewar yana tare da Atiku Abubakar ba sai da na ji yana yi wa masoya Atiku jawabi a zauren taro da ke cikin wani otal a Katsina inda ya ce shi masanin tsimi da tanadi ne, kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya. Atiku Abubakar ne kadai zai iya kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya.
Bincike ya nuna Atiku Abubakar shugaba ne wanda ba shi da kabilanci ko bambancin addini in kun lura ma matarsa ta farko bayarabiya ce Amina Titi Abubakar da kuma Hajjiya Jamila Jennifer Atiku Abubakar ’yar Kkabilar Igbo, saboda haka mu bai wa Atiku Abubakar goyon baya ya zama shugaban kasa dan ya kawar da siyasar danniya, da son zuciya.
Ko kuna sane da Atiku Abubakar ya rasa mahaifinsa tun yana shekara 10, ina nufin a maraya ya taso, yana tafiya makaranta da hawaye saboda tsananin zafin rana da rowan sama, abin da ya sa marigayi mahaifinsa ya ki goyon bayan tafiyarsa makaranta sai wani mutumin kwarai ya kaurar da shi daga Jada zuwa Kojoli da ke Jihar Adamawa a Najeriya, bayan makarantar sakandare da yanzu ake kira Kwalejin Janar Murtala Ramat Mohammed, ya je makarantar kula da tsafta da ke Kano, sai ya mike zuwa Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya karanta fannin aikin shari’a.
Atiku Abubakar tun yana saurayi ya sha faman shiga harkar siyasa kama daga na kungiyoyi har kawo yanzu.
Lallai ne ya dace mu baiwa Atiku Abubakar dama ya zama shugaban kasa da na farfado mana da martabar koguna da muke da su ta wajen samar da madatsun ruwa, saboda a samu wadatar hasken wutar lantarki.
Kada muce za mu yi la’akari da jam’iyyar da ya fito amma mu yi la’akari kan irin taimako da gudunmawarsa ga kasarmu Najeriya, wanda ba za a hada shi da sauran shugabanni ba a fagen juriya da son ya taimaka wa kowa.
Atiku Abubakar mai biyayya ne ga na gaba ku ga irin kukan da ya sha a lokacin da ya samu labarin rasuwar mai martaba Lamidon Adamawa marigayi Alhaji Dr.Aliyu Mustapha, in dai har muka zabi Atiku Abubakar za mu samu kyakkyawan zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Da haka kowa zai yi walwala ba tare da hawaye ko tsoro ba. Ya jama’ar Najeriya mu zaman kwarai nemu ka baiwa Atiku Abubakar da ma ya shugabanci kasar mu Najeriya.
Marubucin dan jarida mai zaman kansa, da ke No. 30 Gambia Crescent, Bekaji Estate, Jimeta Yola, Adamawa State, Jamhuriyar Najeriya.
A tuntubi marubucin kasidar Emmanuel Y. Kwace
Email: [email protected]
Tel: 0805611657, 08034363618
08140022647, 08087721702