Ko yanzu aka yi zaben kananan hukumomin Kaduna za mu lashe – Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar APC na karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Malam Ibrahim Aliyu Koli ya ce ba su tsoron karawa da kowace jam’iyya a zaben kananan hukumomin jihar, kuma ko yanzu aka ce a zo a yi zaben, Jam’iyyar APC ta shirya kuma babu tantama ita ce za ta cinye zaben dukkan kananan hukumomin jihar […]

Ko yanzu aka yi zaben kananan hukumomin Kaduna za mu lashe – Shugaban APC
Ko yanzu aka yi zaben kananan hukumomin Kaduna za mu lashe – Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar APC na karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Malam Ibrahim Aliyu Koli ya ce ba su tsoron karawa da kowace jam’iyya a zaben kananan hukumomin jihar, kuma ko yanzu aka ce a zo a yi zaben, Jam’iyyar APC ta shirya kuma babu tantama ita ce za ta cinye zaben dukkan kananan hukumomin jihar 23.
Malam Ibrahim Aliyu Koli ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilin Aminiya a ofishin jam’iyyar da ke Unguwar Rimi Road a Kafanchan, inda ya ce ko karamar hukuma daya PDP ba za ta samu ba, domin sandar da aka doki uwargida da ita za a doki amarya.
 Shugaban ya ce gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta samu nasarar samar da zaman lafiya a jihar a cikin shekara daya da kama mulkin Jihar Kaduna, ta yadda Musulmi da Kirista suke iya shiga unguwannin da a baya ba sa iya shiga, musamman a kudancin jihar da ya yi kaurin suna wajen rikice-rikicen addini da kabilanci.
“Duk abin da mutum zai yi in babu zaman lafiya, ba zai yiwu ba, a gwamnatocin baya duk da ga sojoji zube a ko’ina a kan hanyoyi, hakan bai hana tashe-tashen hankula ba. Amma zuwan gwamnatin Malam Nasiru el-Rufa’i duk da ba jami’an tsaro a kan hanya sai ga shi an samu sauki saboda ya ce duk wanda ya salwantar da rayuwar wani, ba zai tafi salin-alin ba don haka kowa ya shiga taitayinsa,’’ inji shi.
Ya ce sauran ayyukan da Gwamnan ke yi sun hada da tsabtace garuruwa da ciyar da daliban makarantun firamare wadanda a dalilinsu aka samar da ayyukan yi ga dubban matasa da mata.
Shugaban ya ce gwamnatin kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa a kowane sashi na jihar duk da karancin kudin da ake fama da shi, inda ya yi kira ga jama’ar kudancin Kaduna da suka dauki wata jam’iyya kamar addini su shafa wa kansu ruwa su zo APC a gudu tare a tsira tare don samun ci gaban kudancin Kaduna da jihar da kasa baki daya.