Ko za a iya dora wa mata laifin ingiza mazansu aikata almundahana?

A mafi yawan lokaci za ka ga an kama maza magidanta da laifin almundahana ko wawure makudan dukiya daga ma’aikatarsu. Dalili ke nan wasu ke tunanin cewa matansu na aure ne ke ingiza su, domin su kasance sun azurta iyalinsu, sun rayu cikin facaka da alfahari. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya […]

Ko za a iya dora wa mata laifin ingiza mazansu aikata almundahana?
Ko za a iya dora wa mata laifin ingiza mazansu aikata almundahana?

A mafi yawan lokaci za ka ga an kama maza magidanta da laifin almundahana ko wawure makudan dukiya daga ma’aikatarsu. Dalili ke nan wasu ke tunanin cewa matansu na aure ne ke ingiza su, domin su kasance sun azurta iyalinsu, sun rayu cikin facaka da alfahari. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata ne ke ingiza mazajensu ga yin haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Wasu mazan son ransu ne kawai – Rashida Tiyaye

Hussaini Isah, a Jos

Rashida Tiyaye: ‘’A gaskiya akwai mazan da suke zuwa  su je su aikata miyagun abubuwa kamar sata ko damfara ko cin hanci, don su samu kudi, domin son zuciyarsu kawai, ba wai don mata ne suka  ingiza su ba. Domin babu yadda za a yi mace ta kirki tasa namiji ya je ya yi wani mugun abu, don ya sami kudi ya zo ya biya mata bukata. Amma akwai wasu matan da suke ingiza maza su je su yi abubuwan da ba su dace ba, don su samu kudi su zo su biya masu bukatunsu.”

Laifin ba na mata ba ne – Salisu Adamu

Hussaini Isah, a Jos

Alhaji Salisu Adamu Maikananzir ’Yankaji: ‘’A gaskiya ni ban yarda cewa mata ne suke ingiza maza su je su yi miyagun abubuwa don su sami kudi su zo su biya masu bukata ba. Domin mace ba za ta ce ka je ka dauki bindiga ka yi fashi ko ka yi sata, don ka kawo mata kodi ba. Sai dai kawai in mutum mugu ne ya je ya aikata abin da bai dace ba, ba tare ma da sanin matar da yake tare da ita ba. Domin wasu mata ma ba su san abubuwan da mazajen da suke tare da su suke yi ba. Don haka ni ban yarda cewa mata ne suke ingiza maza su je su yi miyagun abubuwan da ba su dace ba.”

Lallai mata ne ke ingiza maza – Haruna Sabo

Abbas dalibi, a Legas

Haruna Sabo Abdullahi: “A gaskiya mata ne ke yi wa mazajensu ingiza mai kantu ruwa a sha’ani na cin hanci da rashawa. Za ka ga mace ta ce wa mijinta ya saya mata mota iri kaza, ya gina gida irin na wane, duk irin kayayyakin da suka ga wasu matan da su sai su ce su ma sai ka yi masu. Wannan shi ke sanya mazajen tsunduma cikin cin hanci da rashawa, domin su burge matansu saboda wani namijin ma fargabar shiga gidansa yake in bai samo abin da aka dora masa ba. Da haka ne yawanci suke kauce hanya domin su faranta wa matansu rai.”

Kada a dora wa mata laifi – Shahida Ibrahim

Abbas dalibi, a Legas

Shahida Ibrahim Mahmud: “Abin ba haka ba ne, domin mazajen ba su fada wa matansu ta yadda suke samun kudin. Mace ba ta san yadda ya nemo ya ba ta ba, ta yaya za a ce ita ce ta ingiza shi? Son zuciya ne da rashin kishin kasa da kin tsoron Allah suke sanya mazaje cin hanci da rashawa. Ai akwai wadanda duk runtsi ba su yin haka, to ai su ma suna da matan. Don haka mata ba su da hannu a cin hanci da rashawar da mazajensu ke yi.”

Mata na iya jefa maza cikin halaka – Hajiya Rabi

Muhammad Yaba, a Kaduna

Hajiya Rabi Salisu Ibrahim Shugabar kungiyar Arrida Kaduna: “Da gaske ne ana zargin mata da ingiza mazajensu su nemo masu dukiya, wacce ba ta halaliya ba; kasantuwar mata suna da burace-burace ko in ce dan Adam na da dogon buri amma an fi alakanta dogon buri ga mata. Shi ya sa za ka ga namiji ko yana ofis ne ko harkar kasuwanci idan har ba shi da kudi amma yana da mace mai son abin duniya da rayuwa sai ta jefa shi cikin matsala, ta ce ita ga abin da take so ko da karfinsa bai kai ba, sai ya je ya nemo saboda kawai ya faranta mata rai; ko da kuwa ba shi da halin yin haka. Ka ga ke nan idan ya fada cikin halaka ita ce ta zalunce shi, domin ya yi haka ne saboda ya faranta mata rai.”

Bai dace a zargi mata ba – Kwamared Muktar

Muhammad Yaba, a Kaduna

Kwamared Mukhtar Muhammad: “Gaskiya a ra’ayina, bai kamata a zargi mata ba, domin duk mutumin da ka ga yana satar kudin gwamnati da ma can yana da ra’ayin yin hakan ne, domin akwai matan da ke shawartar mazajensu a kan su guji irin wannan mugun hali. Don haka ne nake ganin bai da ce ba a rika zargin mata saboda shi namiji biro ne, ita kuwa mace ruwan biron ne kuma da biro ake abin da ake yi na ba daidai ba.”