Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 1

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin da mutane […]

Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 1
Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 1

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu

zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram

domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya

magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin

da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Anya za su iya kuwa? – Kwamared Ghali
Kwamared Ghali Sulaiman: “Idan har sojoji a karkashin Gwamnatin

Najeriya za su iya murkushe ’yan Boko Haram a cikin makonni shida

kadai da suka kasa yin hakan a cikin shekaru shida da suka wuce, to

ke nan hakan ya nuna tabbacin cewa Gwamnati ce ’yar Boko Haram da ke

yi wa talakawanta ta’addanci.”