Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 3

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin da mutane […]

Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 3
Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 3

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu

zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram

domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya

magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin

da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Makonni shida sun yi kadan – Rabi’u Salisu
Rabi’u Salisu: “Yaudararmu kawai ake so a yi da hakan don kada a yi

zabe, amma batun samar da tsaro a watanni shida ba mai yiwuwa ba ne.

Ya aka yi tsawon shekaru hudu ba su samar da tsaron ba sai yanzu? Sai

da aka ga zabe ya zo sannan za a kawo wannan batu. So dai ake yi a yi

yawo da hankalin talaka. Hadin baki ne kawai da masu mulki don kada a

gudanar da zabe a kasar, sun riga sun gano cewa Janar Buhari ne zai

sami nasara a kansu. Shure-shure dai ba ya hana mutuwa. Muna nan muna

addu’a Allah Ya sa karin lokacin da aka yi ya zama alheri gare mu, mu

samu wadanda ba su shiga APC a da ba su yi amfani da wanann dama su

shiga.”