Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 4
Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin da mutane […]
Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu
zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram
domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya
magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin
da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:]
Za a iya magancewa a mako shida – Salisu Muhammad
Injiniya Salisu Muhammad Gombe: “Ina ganin za a iya magance matsalar
Boko Haram a cikin makonnin shida idan gwamnati ta so kuma idan ya
zama da gaske take yi. Ya za a yi a ce karamar kasa kamar Chadi ta
iya fatattakar ’yan Boko Haram cikin kwanaki biyu amma a ce sun
gagari Najeriya? Wannan ba gaskiya ba ne. Muddin gwamnati ta so
gamawa da mayakan nan kamar yadda ta fada cikin wadannan makonni
shida za ta iya ganin bayansu domin gwamnati ce babu kuma abin da ya
fi karfin gwamnati. Mu dau misali da lokacin mulkin Soja na marigayi
Janar Sani Abacha, inda ya taba gaya wa ’yan Najeriya cewa muddin
yaki ya wuce kwanaki biyu ana yin sa to akwai hannun gwamnati; muddin
ba hannunta kuma a ciki za ta iya kawo karshensa cikin sa’o’i 48. Ka
ga yanzu tunda gwamnati ta ce zata kawo karshensa cikin kankanin
lokaci sai a yi fatan hakan.”