Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:   A yi sulhu […]

Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?
Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi?

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

 

A yi sulhu shi ya fi – Mista Michael Imore

Mista Micheal Imore: “Ni dai a ganina zai fi kyau a zauna da su a sulhunta, maimakon a ce ana amfani da karfin tuwo wajen murkushe su, domin hakan ba zai haifar wa kasar nan, musamman Arewa da mai ido ba. Yanzu dai dubi yadda ake ta kashe mutane, wasu ba su ji ba ba su gani ba. Kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta bi duk hanyar da ta dace domin gano wadannan mutanen kuma a zauna da su.
“Yanzu da aka sulhunta da ’yan tsagerun Neja-Delta, ba an dan samu sauki ba? Ni ban yarda karfi na iya kawo karshen wannan matsalar da wadannan mutanen ke haifarwa ba, domin an dade ana amfani da karfi amma har yanzu an kasa shawo kan matsalar”

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu