Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 1

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:   Da karfi zai […]

Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 1
Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 1

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

 

Da karfi zai magani da tuni an gama – Jamilu Lawal

Jamilu Lawal: “Ba na tsammani cewa karfin tuwo na iya kawo karshen Boko Haram. Tun yaushe ake dauki ba dadi da su kuma har yau an kasa shawo kan al’amarin? Kuma kar ka manta cewa su fa har yanzu ba a san su ba, ana kai farmakin kan mai uwa da wabi ne kuma duk da kashe sun da ake yi yau shekaru 3 koma fiye amma har yanzu yi ake yi kamar ba a yi. Don haka ni a ganina, karfin tuwa ba zai yi magani ba.
“Kuma su sun san inda abokan gaban su suke amma abokan gaba ba su san inda suke ba. Don haka ni a ganina, matakin nan na farko da aka dauko, wato neman sulhu da su shi ne ya fi amfani.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi