Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 2

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:   Addu’a ce kawai […]

Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 2
Ko za a iya magance matsalar Boko Haram ta amfani da karfi? 2

Ya zuwa yanzu, duk wasu matakai da aka dauka don murkushe matsalar Boko Baram ba su biya bukata ba. A yanzu an tsaya ga amfani da karfi kadai. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko amfani da karfi zai magance matsalar? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

 

Addu’a ce kawai magani – Alhaji Shu’aibu

Alhaji Shu’aibu Garun Malam: “Dokar ta baci da kwamitoci duk ba su da amfani, gara a rusa su a nemi maslaha, a daina takura wa mutane, a dawo masu da sadarwa shi ne mafi alheri. Don ko yakin duniya da yakin Biyafara duk bayan an gama wuta dole sai da aka hau teburin sulhu. To ina dalilin da ba za a yi haka ba, a nemi matasa da shugabannin al’umma a hada kai da su a magance lamarin? Kudin da ake kashewa na ’yan watanni sun kai a daidaita wannan magana kamar yadda aka yi da matasan yankin Neja-Delta.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi